Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

00:00
00:00

Avsnittssammanfattning

Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa ya sake leƙawa ƙasar Togo a wannan mako, inda ya duba yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa.

Avsnitt

404-

Yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa a ƙasar Togo

Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa ya sake leƙawa ƙasar Togo a wannan mako, inda ya duba yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa.

11 Nov 2026
403-

Mahukunta na yunkurun sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Nijar

Shirin Al'adun Mu Na Gado na wannan mako yayi duba ne kan yunƙurin sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Niger da magabatan ƙasar suka dauri aniyar yi. Tun bayan juyyin milki da sojojin ƙasar Niger suka yi da niyar raba gari da suka yi da duk wani gadon Turawan mulkin mallaka da suka mullaki ƙasar, sun ga dacewar sake rubuta tarihin ƙasar domin galibinshi tarihi ne da Turawan suka rubuta abinda yayi musu, wanda wani lokacin ma ba gaskiya bane ko kuma an masa gyaran fuska. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa...............

27 Okt 2026
402-

Yadda al'ummar Hausawa kusan dubu 30 ke rayuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar Togo

Shirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya tsakanin su ba tareda an fuskanci wata matsala. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdoulaye Issa................

20 Okt 2026
401-

Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar

'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.

13 Okt 2026
400-

Mahukuntan Nijar sun karrama fitaccen mawaƙin gargajiya Mamman Gawo Filinge

Da yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa. Mawaƙin ya taka gagarumar rawa sakamakon waƙokinsa na siyasa da na gargajiya, da noma da kuma zamantakewa, lokacin da ya yi zamaninsa a shekarun 1960 zuwa 1980. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

06 Okt 2026